‘Ba zan taɓa mantawa da juyin mulkin da aka yi wa Shagari ba’
Uwargidan tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Hajiya Maryam Abacha ta ce Janar Sani Abacha, jajirtaccen shugaba ne kuma tsayayye da bai lamunci sakaci da taɓarɓarewar al’amura a ƙasa zamanin mulkinsa ba.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi mulki ne daga 1993 zuwa 1998 inda ya yi ƙoƙarin mayar da Najeriya kan mulkin dimokraɗiyya a lokacin da ƙasar ke cikin rashin kwanciyar hankalin siyasa sanadin dambarwar 12 ga watan Yuni (June 12).
Maryam Abacha ta ce maigidanta ya yi ƙoƙarin daidaita harkoki a ƙasar, da dawo da kwanciyar hankali a zamaninsa saɓanin abubuwan da ke faruwa a yanzu.
Ta bayyana haka ne yayin zanytawa ta musamman da BBC Hausa albarkacin cikar maigidanta shekara 25 da rasuwa.
Janar Abacha na cikin jerin shugabannin Najeriya da suka rasu a kan mulki.
Ta ce miyagun maganganun da ake yaɗawa a kan marigayi Sani Abacha, ba su da tushe, don kuwa ba a ga taɓarɓarewar harkokin mulki a zamaninsa ba.
An dai yi ta zargin tsohon mulkin sojan da zama ɗan kama-karya da ƙarfa-ƙarfa ga kuma wawashe dukiyar ƙasa, don azurta kansa.
Sai dai Maryam Abacha ta ce: “Yanzu me ke faruwa a (jihohi kamar) Kano? Me ke faruwa a ƙasa? Ai su ne maganganu marasa kyau, zamaninmu an yi wa’yannan ne duka? Ai ba a yi su ba!”
Uwargidan tsohon shugaban ƙasar ta ce cikin abubuwan da ba za ta taɓa mantawa da su ba, a tsawon rayuwarta da Janar Abacha musamman lokacin aikinsa na soja, shi ne juyin mulkin tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari.
Maryam Abacha ta ce a wannan lokacin, ta farka cikin wata safiya, sai ta fahimci cewa tun tsakar dare maigidanta ya sa kakin soja ya fita.
“Sai na ce me ke faruwa a ƙasar, me ke faruwa a gari da ba mu ji ba, ba mu sani ba?
Out of tunani, sai na je na ɗau rediyo na kunna”.
Uwargidan marigayin ta ce a lokacin ne ta ji ana ta kaɗa badujalar soja kafin daga bisani ta ji muryar “maigida”.
Ta ce bayan ta sake sauraro ne ta ji saƙon da yake isarwa. “Gaskiya ran nan na firgita sosai don gaskiya ban ji daɗi ba”.
A cewar Maryam Abacha sai can daga baya ne suka fahimci cewa juyin mulki sojoji suka yi. Kuma ba a sanar da sabon shugaban ƙasa ba sai bayan ƙarfe 12n dare inda aka bayyana sunan Janar Buhari a matsayin babban hafsan da ya hau kan karagar mulki.
“Lokacin ma ba su zo gida ba, ko sai bayan kwana huɗu ne?” To wannan lokacin gaskiya akwai tashin hankali da tsoro da kuma ɓacin rai.
Ba na kewar Villa – Maryam Abacha
Maryam Abacha ta ce ba ta kewar komai a fadar shugaban ƙasa ta Najeriya.
A cewarta, fadar shugaban ƙasa wato Villa duk da yake akwai ɗaukaka amma kuma tana cike da matsaloli.
Ta ce a tsawon aikin maigidanta, Janar Sani Abacha ba ta za iya ƙirga gidajen da suka zauna ciki ba. “Babana ma ma’aikacin gwamnati ne, so muna ta yawo daga gari yana canza gari, har aka yi min aure.
To, ko gidan soja ma kullum, yau kana nan, (sai) a canza a kai ka can”.
Mutuwar Abacha ta bagatatan ta ɗimauta Najeriya
Janar Sani Abacha ya rasu ne a ranar 8 ga watan Junin 1998.
Rasuwarsa kuma ta ɗimauta ƙasar musamman ganin ba wata jinya ya yi ba.
Uwargidansa Maryam Abacha ta ce iyalinsa na yi wa marigayin addu’o’i a duk ranar zagayowar mutuwarsa.
“Muna addu’o’i da mu da mutanen gida da limamanmu, muna fidda’u, muna mishi addu’o’i,” a cewarta.
Hajiya Maryam Abacha ta kuma ce rayuwarsa da iyalinsa ta sha banban da aikinsa na soja.
A cewarta marigayin mutum ne mai son yin raha da iyalinsa da kuma motsa jiki.
“Zai tashi da safe ya yi ibada, ya yi addu’o’i kafin ya shirya ya tafi wurin aiki”, in ji ta.
Rayuwar marigayi Sani Abacha
A ranar 20 ga watan Satumban 1943 aka haifi Sani Abacha a Kano.
Ya yi makarantar firamari ta City Senior Primary School, Kano sannan ya tafi zuwa sakandiren Government College, Kano a 1957-1962.
Ya halarci Kwalejin horas da sojoji ta Kaduna daga 1962-1963 kafin ya wuce kwalejin Horas da Sojoji ta Aldershot da ke Ingila a 1963. Ya kuma samu horo a a Kwalejin Horas da Dakarun ƙasa ta Warminster da ke Birtaniya a 1966.
A 1971 a halarci kwalejin sojoji ta Jaji da ke Kaduna har zuwa1976.
Sannan ya je kwalejin tsara manufofi da dabarun mulki ta Kuru da ke Jos a 1981.
Ya yi kuma wasu kwasa-kwasai da suka shafi harkar tsaro a Kanada da Amurka a 1982.
Ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya
A ƙarƙashin mulkinsa ne asusun kuɗaɗen wajen Najeriya ya ƙaru daga dala miliyan 494 a 1993 zuwa dala biliyan 9.6 a tsakiyar 1997.
Tsohon shugaban mulkin sojan ya yi ƙoƙarin rage bashin da ake bin ƙasar daga dala biliyan 36 a 1993 zuwa dala biliyan 27.
Mutuwarsa
A ranar 8 ga watan Yunin 1998, Janar Sani Abacha ya rasu a fadar shugaban ƙasa.
Ga wasu ‘yan Najeriya marigayi Sani Abacha, shugaban ƙasa ne da ya taka rawar gani wajen kawo ci gaba.
Wasu kuwa na kallonsa a matsayin ɗan mulkin kama karya.