close
close

Wane tasiri ne zaɓen Turkiya zai yi ga ƙasashen duniya?

Wane tasiri ne zaɓen Turkiya zai yi ga ƙasashen duniya?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu zaɓe a wani gangamin adawa

Idan har shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya faɗi zaɓe a ranar 28 ga watan Mayu, za a iya samun sauyi na mu’amular ƙasar da ƙasashen duniya.

Ƙarƙashin shugabancin Erdogan, Turkiyya ta fusata aminanta ƙasashen yammani saboda amincinta da Rasha. Ya kuma aike da dakarun Turkiyya a rikicin Iraƙi da Syria da Libya.

Ɗan takarar adawa Kemal Kilicdaroglu, ya yi alƙawalin zama babban mai da’awar muradun ƙasashen yammaci.

Ya Turkiyya za ta yi da ƴan gudun hijirar Syria?

Akwai kimanin ƴan Syria miliyan 3.7 da ke cikin Turkiyya, waɗanda suka gujewa yaƙi a ƙasarsu – da kuma wasu ƴan gudun hijira na wasu ƙasashe kamar Afghanistan.

  • May 27, 2023